Dakarun Khalifa Haftar sun kai hari a tashoshin Man fetur din kasar
Sojojin dake biyayya ga Khalifa Haftar sun fara kai a tsibiran yankin Hilal mai arzikin Man fetur
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto Ali Alhisa kakakin Dakarun dake tsaron cibiyoyin Man fetur din kasar Libiya na cewa a wannan Lahadi Sojojin dake biyayya da Khalifa Haftar sun fara kai farmaki a tsibiran Zawutina, Ra'as Lanuf, Sadir da kuma garin Ajdabiya inda yanzu haka rahoton ke cewa ana can ana gwabza fada da masu tsaron wadannan ciboyoyi.
A bangare guda, mai magana da yawun Sojojin dake biyayya da Khalifa Haftar Ahmad Mismari ya bayyana cewa sun kwace tsibiran La'as Lanuf, Sadir da kuma Barka.
Daya daga cikin Injiniyoyin dake aiki a wadannan tsibirai ya bayyana cewa Dakarun Khalifa Haftar sun banka wuta a runbun tsimi Man fetur na tsibirin Sadir.
Tun a shekarar 2014 aka rufe tashohsin tsibiran Ra'as Lanuf da Sadir, amma a cikin yan watanin da suka gabata masu kula da wadannan tashoshi tare da hadin gwiwar Gwamnatin hadin kan 'yan kasar dake ta samu goyon bayan MDD sun sake bude su domin ci gaba da jigilar Danyan Man kasar zuwa kasuwanin Duniya.