Khalifa Haftar Ya Fayyace Dalilin Mamaye Cibiyoyin Man Fetur Na Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11047-khalifa_haftar_ya_fayyace_dalilin_mamaye_cibiyoyin_man_fetur_na_kasar_libiya
Kwamandan rundunar sojin gwamnatin Libiya da ke gabashin kasar Khalifa Haftar ya yi suka kan damuwar da kasashen yammacin Turai suka nuna dangane da mamaye cibiyoyin man fetur na kasar Libiya da sojoji masu masa biyayya suka yi.
(last modified 2018-08-22T06:58:55+00:00 )
Sep 14, 2016 12:15 UTC
  • Khalifa Haftar Ya Fayyace Dalilin Mamaye Cibiyoyin Man Fetur Na Kasar Libiya

Kwamandan rundunar sojin gwamnatin Libiya da ke gabashin kasar Khalifa Haftar ya yi suka kan damuwar da kasashen yammacin Turai suka nuna dangane da mamaye cibiyoyin man fetur na kasar Libiya da sojoji masu masa biyayya suka yi.

Janar Khalifa Haftar kwamandan rundunar sojin gwamnatin Libiya da ke gabashin kasar da duniya ta janye goyon bayan da take mata bayan kafa gwamnatin hadin kan kasa a birnin Tripoli a yau Laraba ya bayyana cewa: Kwace iko da cibiyoyin man fetur da sojoji masu yi masa biyayya suka yi lamari ne da baya da alaka da siyasa ko nuna adawa da gwamnatin hadin kan kasa da ke birnin Tripoli ko kuma kokarin bakanta ran wata kasa, iyaka dai yunkuri ne na kare cibiyoyin man daga fadawa muggan hannu.

Khalifa Haftar ya kara da cewa: Kungiyoyin tsoffin 'yan tawayen Libiya ne suke mamaye da cibiyoyin man tare da cin karensu babu babbaka a harkar man, don haka ya zame wajibi a kakkabe hannunsu daga harkar man fetur da ke matsayin arzikin kasar Libiya.