An Kame Daya Daga Cikin Kwamandojin Da'esh A Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11128-an_kame_daya_daga_cikin_kwamandojin_da'esh_a_libya
An Kame Rabi'u Hussain al-Hawary, kwamandan Da'esh a kasar Libya.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 16, 2016 14:27 UTC
  • An Kame Daya Daga Cikin Kwamandojin Da'esh A Libya

An Kame Rabi'u Hussain al-Hawary, kwamandan Da'esh a kasar Libya.

An Kame daya daga cikin kwamandojin kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a garin Darhan na kasar Libya mai suna  Rabi'u Hussain al-Hawary.

Jaridar Yau al-Sabiu da ake bugawa a kasar Masar ta ce an kame  kwamandan na Da'esh na garin Darnah, a jiya alhamis ne bayan da jami'an tsaro su ka bi sawunsa a garin Ajdabiyah.

Majiyar tsaron kasar ta ci gaba da cewa; Rabiu Hussain al-Hawary, ya yi takardun shiga da fice na bogi da zummar ficewa daga kasar suwa kasar Masar.

Gwamnatin hadin kan kasa ta Libya tana samun galaba akan kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin fadin kasar.