An Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Halifa Haftar A Kasar Libiya
Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar al'ummar kasar sun gudanar da wata zanga-zangar nuna goyon bayansu ga sojojin kasar da suke gabashin kasar karkashin jagoranci Janar Halifa Haftar da kuma nuna rashin amincewarsu da tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin cikin gidan kasar.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na Iran ya bayyana cewar dubun dubatan mutane a garuruwa daban-daban na kasar Libiyan ne suka gudanar da zanga-zangogi don nuna goyon bayansu ga nasarorin da sojojin kasar karkashin jagorancin Janar Halifa Haftar din suka samu na kame yankunan bakin ruwa inda cibiyoyin man fetur na kasar suke, suna masu kiran Amurka da sauran kasashen turai da su fice daga yankin Al-Hilal mai arzikin man fetur na kasar.
Rahotannin sun ce an gudanar da wadannan zanga-zangogin ne a ranar tunawa da zagayowar ranar da 'yan mulkin mallakan Italiya suka kashe jagoran gwagwarmayar fada da 'yan mulkin mallaka na kasar Sheik Umar Mukhtar.