Tashin Bom ya hallaka Mutane 4 A arewacin kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11437-tashin_bom_ya_hallaka_mutane_4_a_arewacin_kamaru
Majiyar kasar Kamaru ta sanar da mutuwar Mutane 4 sanadiyar harin kunar bakin wake a wani yanki dake arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 23, 2016 02:21 UTC
  • Tashin Bom ya hallaka Mutane 4 A arewacin kamaru

Majiyar kasar Kamaru ta sanar da mutuwar Mutane 4 sanadiyar harin kunar bakin wake a wani yanki dake arewacin kasar

Harin ya auku ne da misalin karfe takwas na daren Laraba a yankin Djakana mai nisan kilomita 5 da iyakar kasar da Najeriya , daga cikin Mutane 4 da suka rasu uku fararen hula ne dayan kuwa dan kunar bakin waken ne.har ila yau harin ya yi sanadiyar jikkatar fararen hula da dama wasu daga ciki na cikin mawuyacin hali.

Rahoton ya ce yankin na Djakana ya fuskancin hare-haren kungiyar boko haram da dama, inda a ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata ma aka kai wani mumunan harin kunar bakin wake a yankin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 11.