EU Ta Tsawaita Takunkuminta Ga Kakakin Majalisar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11821-eu_ta_tsawaita_takunkuminta_ga_kakakin_majalisar_libiya
Kungiyar tarayya turai (EU) ta tsawaita takunkumin data kakabawa wasu manyan jami'an Libiya su guda uku ciki har da kakakin majalisar dokokin Tobruk, Aguila Saleh, bisa zarginsu da kawo cikas ga yunkurin samar da zamen lafiya a wannan kasa.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 01, 2016 07:12 UTC
  • EU Ta Tsawaita Takunkuminta Ga Kakakin Majalisar Libiya

Kungiyar tarayya turai (EU) ta tsawaita takunkumin data kakabawa wasu manyan jami'an Libiya su guda uku ciki har da kakakin majalisar dokokin Tobruk, Aguila Saleh, bisa zarginsu da kawo cikas ga yunkurin samar da zamen lafiya a wannan kasa.

Takunkumin dai ya shafi hana mutanen taba kaddarorinsu da kuma tafiye-tafiye tsakanin kasashen membobin kungiyar.

Sauren mutanen biyu da takunkumin ya shafa sun hada da Khalifa al-Ghweil da Nuri Abu Sahmein dukkansu masu adawa da gwamnatin hadakar.

EU ta tsawaita takunkumin ne da wattanni shida wanda zai kai har zuwa watan Afrilu na shekara mai zuwa.

Majalisar dokokin Tobruk, ita ce wace duniya ta amunce da ita, saidai a watan Agusta taki amuncewa da gwamnatin hadaka ta (GNA) dake samun goyan bayan MDD.