Sansanin IS na birnin Bangazi ya koma kalkashin Sojijn kasar Libiya
Dakarun kasar Libiya Sun samu nasarar kwahse Babban sanasanin 'yan ta'addar ISIS na Birnin Bangazi dake gabashin kasar
Kafar watsa labaran Rusia Alyaum ta nakalto Fadlu Alhasi babban kwamandan rundunar kasar ta musaman wacce aka bata taken Alsa'ika a yau na cewa Dakarun tsaron kasar sun samu nasarar tsarkake yankin Allaisi na birnin Bangazi dake a matsayin babban sansanin 'yan ta'addar IS baki dayansa daga hanun 'yan ta'addar.
Alhasi ya kara da cewa Dakarun tsaron kasar sun kai sumame kai tsaye a sansanin 'yan ta'addar dake wannan yanki inda suka hallaka wani adadi mai yawa daga cikinsu, wasunsu kuma suka ramta a na kare.
Bisa wannan rahoton Sojojin na Libiya sun samu nasarar buda tsohuwa da sabuwar hanyar dake kaiwa zuwa ga yankin na Laisi.
Baya ga wannan nasara, A cikin 'yan kwanakin nan Dakarun tsaron Libiya sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'addar ISIS daga yankin Alhawari , tsibirin Almarisa dake kudancin Bangazi tare da kuma da kame makaman 'yan ta'addar masu yawa.