Libiya : Anyi Gumurzu Tsakanin (IS) Da Sojoji A Sirte
Rahotanni daga Libiya na cewa sojojin kasar takwas ne suka rasa rayukansu a yayin wani gumurzu tsakaninsu da mayakan (IS) a birnin Sirte dake zamen sansanin 'yan ta'addan na Da'esh.
Yau dai kusan watanni biyar kenan da dakarun gwamnatin hadaka na Libiya ke kokarin kwace wannan birnin na Sirte daga hannun 'yan ta'addan.
Wata sanarwa daga gwamnatin ta ce sojojinta na ci gaba da kutsa kai a yankin da nufin tsarkake shi daga duk wata barazana kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa dakarun gwamnatin kasar sunyi nasara hallaka 'yan ta'addan goma.
Dakarun gwamnatin hadaka sunyi nasara kwato daukacin birnin dake nisan kilomita 450 daga gabashin Tripoli babban birnin kasar, saidai tun soma fadan sama da dakarun kasar 450 ne suka sara rayukansu kana wasu 2,500 suka raunana, saidai har kawo yanzu babu alkalumen yawan 'yan ta'addan da aka kashe a tsawan wannan lokaci.