Rikicin Kasar Libiya Yana Ci Gaba Da Lashe Rayukan fararen Hula
Hari da makami mai linzami ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula akalla uku tare da jikkata wasu goma sha biyu na daban a garin Benghazi da ke arewacin kasar Libiya.
Kamfanin dillancin labaran Reuters a jiya Talata ya habarta cewa: Hari da makami mai linzami ya fada kan gidajen fararen hula a garin Benghazi da ke arewacin kasar Libiya, inda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula akalla uku tare da jikkata wasu goma sha biyu na daban.
Majiyar rundunar sojin Libiya karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar da take fada da kungiyoyin tsoffin 'yan tawayen Libiya a garin Benghazi ta daura alhakin hari kan gidajen fararen hula a kan kungiyoyin 'yan ta'adda.
Tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011, kasar Libiya ta tsunduma cikin matsalar tashe-tashen hankula sakamakon bullar kungiyoyin 'yan ta'adda musamman kungiyar ta'addanci ta Da'ish da ta mamaye garin Sirt.