Kamaru : Mutane 55 Suka Mutu A Hadarin Jirgin Kasa
Oct 22, 2016 06:16 UTC
A kasar kamaru adaddin mutanen da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin kasa ya kai 55, a yayin da wadanda suka raunana ya kai kusan 600.
Hadarin dai ya auku ne jiya Juma'a a lokacin da jirgin ya kauce hanya a lardin Eseka dake tsakanin biranen Yaounde da Duala a cewar ministan sufuri na kasar Edgar Alain Mebe Ngo'o.
Kimanin taragai 11 ne suka jirkice bayan da jirgin ya kauce hanya.
Har kawo yanzu dai ba'a kai ga tabbatar da sanadin hadarin ba.
Bayanai daga kasar sun nuna cewa mutane da dama ne suka yi amfani da jirgin kasan a wannan ranar saboda katsewar gadar dake hada mayen biranen kasar biyu.
Tags