Libya: An 'Yanto Fursunonin Da Su ke hannun Da'esh A Kasar Masar
"Yanto Fursunoni Daga Hannun Daesh
Sojojin Kasar Libya Sun kwato wasu mutane da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh, ( isil) ta yi garkuwa da su a garin Sirt.
Kamfanin dillancin Labarun Reuters ya ambato kakakin sojojin kasar ta Libya, Rida Isa yana cewa; Sojojin sun kwato mata 11 'yan asalin kasar Eriteria da dan kasar Turkiya guda da kuma wani Bamisre da 'yan ta'addar Da'esh ta yi garkuwa da su.
Watanni 6 kenan dai da sojojin kasar ta Libya su ka shelanta yaki akan kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh da ta ke rike da birnin Sirt.
Kawo ya zuwa yanzu dai sojojin kasar ta Libya sun kwace wasu yankuna na birnin, sai dai har yanzu 'yan ta'addar na Da'esh na rike da shi ta hanyar amfani da kwararrun maharba da su ke kan tuddai da dogayen gini.