Kamaru : Mutane 79 Suka Mutu A Hadarin Jirgi Kasa
A kasar Kamaru adadin mutanen da mutu a hadarin jirgin kasa a ranar Juma'a data gabata ya kai 79.
A wata sanarwa da aka fitar ta gidan radio na kasar wato (CRTV) an ce adaddin ya karu ne bayan samun wasu gawarwwakin mutane 11 a jiya Lahadi.
Haka zalika a cewar sanarwar yawan mutanen da suka raunana a yayin hadarin ya kai 551, kuma mafi yawancinsu a garzaya dasu a gidajen asibitocin gwamnatin dake Duala.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin kasar ke gudanar da zaman makoki a yau Litinin domin juyayin mutuwar mutanen da mummunan hadarin ya rusa dasu.
Hadarin dai ya auku ne ranar Juma'a data gabata a lokacin da jirgin ya kauce hanya a lardin Eseka dake tsakanin biranen Yaounde da Duala inda tazagai kimanin 11 suka jirkice.
Har kawo yanzu dai ba'a kai ga gano sanadin hadarin jirgin ba.