An Gano Gawawakin Bakin Haure 16 A Gabar Ruwan Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13147-an_gano_gawawakin_bakin_haure_16_a_gabar_ruwan_libya
Rahotanni daga Libya na cewa an samo gawawakin wasu bakin haure 16 a gabar ruwan kasar, wadanda bisa ga dukkan alamu sun rasa rayukansu a akokarin tsallakawa ta tekun bahar Rum domin zuwa turai.
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 30, 2016 12:28 UTC
  • An Gano Gawawakin Bakin Haure 16 A Gabar Ruwan Libya

Rahotanni daga Libya na cewa an samo gawawakin wasu bakin haure 16 a gabar ruwan kasar, wadanda bisa ga dukkan alamu sun rasa rayukansu a akokarin tsallakawa ta tekun bahar Rum domin zuwa turai.

Da yake tabbatar da hakan kakakin hukumar bada agaji yankin, Khames el-Boussefi ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP, cewa an gano gawawakin ne a bakin teku a lardin Zouara dake nisan kilomita 160 daga yammacin birnin Tripoli a iyaka da kasar Tunisiya.

Ya kara da cewa ba'a kai ga tantance 'yan asalin wace kasa ne ba, aman ya ce bisa ga alamu sun mutu ne bayan da kwale kwalensu ya nutse a teku.

tuni dai a cewarsa aka mika gawawakinbakin hauren ga hukumomi wadanda keda nauyin jana'izarsu.

Bakin haure da dama ne dai ke amfani da rikicin da kasar Libiya ta tsunduma tun bayan kifar da mulkin Mua'ammar Ghaddafi a shekara 2011 domin kwarara turai ta tekun bahar rum.

Alkaluman da hukumar kula da kaurar bakin haure ta MDD ta fitar sun nuna cewa bakin haure kimanin 3,800 ne suka rasa rayukansu ko suka bace a tekun bahar rum a kokarin tsallakawa Turai da zumar samun rayuwa mai inganci, wanda adadin kuma a cewar hukunar ta OIM shi ne mafi girma a tarihi.