Mayakan Boko Haram Sun Kai Farmaki A Arewacin Kasar Kamaru
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wani hari a arewacin kasar Kamaru a jiya litinin sun kuma jawo mutuwa da raunata mutane da dama.
Shafin yanar gizo na Africa Times ya nakalto majiyar jami'an tsaron kasar Kamaru tana cewa an kai harin ne a garin Kangarwa kusa da garin Mora a arewacin kasar, kuma harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3 da kuma raunata wasu 6. Majiyar ta kara da cewa mayakan na boko haram sun kuma kona wasu gidaje a garin sannan suka arce zuwa cikin tarayyar Nigeria.
Duk da cewa sojojin kasar Kamaru sun sami nasarar dakile wasu hare hare masu yawa na boka haram din a baya amma a wannan karon mayakan na boko haram sun yaudaresu kafin su kai ga harin da suka kai garin na Kangarwa a jiya.
Kungiyar yan ta'adda masu kafirta mutane ta Boko Haram dai ta fara daukar makamai ne tun shekara ta 2009 kuma ya zuwa shekara ta 2015 ta kashe mutane akalla dubu 20 a cikin kasashen Nigeria kamaru Chadi da kuma Niger.