An tsarkake garin Sabrata daga hanun IS
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1342-an_tsarkake_garin_sabrata_daga_hanun_is
A kwato garin Sabrata dake yammacin Libiya daga hanun 'yan ta'addar IS.
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 27, 2016 02:08 UTC
  • An  tsarkake garin Sabrata daga hanun IS

A kwato garin Sabrata dake yammacin Libiya daga hanun 'yan ta'addar IS.

Tashar Talabijin ta Almayadin da ke kasar Labanan ta habarta cewa, ma'aikatar tsaron gwamnatin Tripoli da bata samun goyon bayan kasashen duniya ta sanar da fatattakar 'yan t'addan ISiS daga garin Sabrata.

A baya dai , Kungiyar ta IS ta gudanar da wani shiri na kafa gwamnati a garin Sabratan da yake a matsayin cibiyar samar da iskar Gas din kasar mai nisan kilomita 70 daga yammacin Tripoli babban birnin kasar.

Bayan kwashe shekaru biyar da yin juyin juya halin kasar Libiya, har yanzu Al'ummar kasar ba su samu sukuni ba, sai ma yadda kasar ke ci gaba da fadawa cikin mawuyacin hali, inda kasar ke fuskantar kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban da suka tare a kasar daga kasashen duniya.

Kungiyar 'yan ta'addan ISIS mai fafutukar kafa daular musulnci ta mamaye wasu yankuna a cikin kasar.

Yanzu haka dai kasar ta Libiya nada gwamnati da majalisar dokoki guda biyu, daya a babban birnin wato Tripoli, dayar kuma ita ce wacce hedikwatarta ke birnin Trabruk dake gabashin kasar, wadda kuma ita ce duniya ta amince da ita.