Nakiya Ta Hallaka Wani Sojin Faransa A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13426-nakiya_ta_hallaka_wani_sojin_faransa_a_mali
Wani sojin faransa ya rasa ransa a yayin da motar da suke ciki ta taka nakiya a arewacin Mali inda gungun mayakan dake da'awar jihadi ke ci gaba da kasancewa duk da yerjejeniyar sulhun da aka cimma a shekara 2015 data gabata.
(last modified 2018-08-22T06:59:11+00:00 )
Nov 05, 2016 13:09 UTC
  • Nakiya Ta Hallaka Wani Sojin Faransa A Mali

Wani sojin faransa ya rasa ransa a yayin da motar da suke ciki ta taka nakiya a arewacin Mali inda gungun mayakan dake da'awar jihadi ke ci gaba da kasancewa duk da yerjejeniyar sulhun da aka cimma a shekara 2015 data gabata.

Tuni dai kungiyar Ansar Din ta Iyad Aghali dake da alaka da kungiyar 'yan ta'addan Alaida ta dauki alhakin kai harin a wata sanarwa data wallafa a shafin ta na Internet, saidai ba tare da wani karin bayyani ba, saidai cewar harin ya auku ne a nisan kilomita 60 daga birnin Kidal.

Kafin hakan wata sanarwa da ma'aikatar tsaron faransa ta fitar ta ce wasu motocin tawagar sojojin kasar a mali wato (Barkhane) sun gamu da harin wani abu mai fashewa a arewa maso gabashin Kidal. 

Harin da a cewar sanarwar yayi sanadin mutuwar Marshal Fabien Jacq, tare da raunana wani sojin.

Wannan dai ya sanya adadin sojojin faransa da suka mutu a kasar ta Mali zuwa 16 tun dai lokacin da suka sanya kafa a arewacin kasar ta Mali a watan janairu na shekara 2013 da nufin yaki da masu tsatsauren ra'ayin addini.