Libya: An tseratar da Fararen Hula 14 Daga Hannun Da'esh
Sojojin kasar Libya Sun Kwato fararen hula daga hannun kungiyar Da'esh
Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato cewa; Sojojin Libya sun 'yanto da fararen hula 14 bayan da su ka yi nasarar kwace wane yanki a garin sirt da ya ke a hannun kungiyar Da'esh.
Garin na Sirt mai mutane dubu tamanin, ( 80.000) ya shiga hannun kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ne a watan Aprilu na 2015. Bayan kafa gwamnatin hadin kan kasa a cikin watan Yuni na wannan shekarar da ake ciki ne dai sojojin kasar su ka fara kai farmaki da zummar kwato shi daga hannun 'yan ta'adar.
A cikin garin na Sirt, kwararrun maharban 'yan ta'adda da kuma nakiyoyi da aka dasa, suna kawo wa sojoji cikas da hana su kwace garin cikin sauri.