Mahukuntan Kasar Kamaru Sun Kame 'Yan Kungiyar Boko Haram Masu Yawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1366-mahukuntan_kasar_kamaru_sun_kame_'yan_kungiyar_boko_haram_masu_yawa
Majiyar tsaron kasar Kamaru sun sanar da cewa; Jami'an tsaron kasar sun gudanar da wani samame a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke cikin kasar, inda suka yi nasarar kame 'yan kungiyar Boko Haram masu tarin yawa.
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 27, 2016 06:43 UTC
  • Mahukuntan Kasar Kamaru Sun Kame 'Yan Kungiyar Boko Haram Masu Yawa

Majiyar tsaron kasar Kamaru sun sanar da cewa; Jami'an tsaron kasar sun gudanar da wani samame a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke cikin kasar, inda suka yi nasarar kame 'yan kungiyar Boko Haram masu tarin yawa.

Shafin Afirka Time ya habarto daga majiyar tsaron kasar Kamaru cewa; Jami'an tsaron kamaru sun gudanar da wani samame a sansanin Tcharkamari da ke arewacin kasar kusa da kan iyaka da Nigereiya, inda suka yi nasarar gano 'yan kungiyar Boko Haram 14.

Jami'an tsaron Kamaru sun tsananta gudanar da samame ne a yankunan kasar da suke iyaka da tarayyar Nigeriya sakamakon jerin hare-haren ta'addanci da mayakan kungiyar Boko Haram suke kai wa cikin kasarsu a 'yan makonnin nan.