Daruruwan 'Yan Boko Haram Sun Mika Kai Ga Sojojin Kasar Chadi
(last modified Sat, 12 Nov 2016 16:50:23 GMT )
Nov 12, 2016 16:50 UTC
  • Daruruwan 'Yan Boko Haram Sun Mika Kai Ga Sojojin Kasar Chadi

Majiyoyin tsaron kasar Chadi da na MDD sun bayyana cewar daruruwan 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram sun mika kansu tare da iyalansu ga jami'an tsaron kasar Chadin cikin watan da ya gabata a wani abin da ake ganinsa a matsayin irin nasarar da ake ci gaba da samu a kansu.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo mai magana da yawun dakarun hadin gwiwa da ke da (MNJTF) da ke da helkwata a birnin N'Djamena Kanar Muhammad Dole yana cewa 'yan Boko Haram din sun mika kan da dakarun hadin gwiwan a kusa da Tekun Chadi.

Kanar Dole ya ci gaba da cewa, dakarun Boko Haram din suna ci gaba da mika kai ne sakamakon irin wutar da suke fuskanta daga wajen dakarun hadin gwiwan, yana mai cewa tun daga watan Satumbar da ya gabata dakarun Boko Haram din suke ci gaba da zuwa tare da makamansu suna mika kansu.

Kakakin rundunar hadin gwiwan ya kara da cewa ya zuwa yanzu akwai kimanin 'yan Boko Haram din 240 tare da iyalansu, mafiya yawansu 'yan ksar Chadi, da ake tsare da su a wajajen da sojojin suke tsare wadanda suka kama.

Cikin watannin baya-bayan nan dai dakarun hadin gwiwan na kasashen yankin suna ci gaba da yakan 'yan Boko Haram din da nufin kawo karshen ayyukan ta'addancin kungiyar.