Jaddadawar Kungiyar Tarayyar Afirka Kan Wajibcin Fada Da Kungiyar Boko Haram
(last modified Mon, 14 Nov 2016 05:53:28 GMT )
Nov 14, 2016 05:53 UTC
  • Jaddadawar Kungiyar Tarayyar Afirka Kan Wajibcin Fada Da Kungiyar Boko Haram

A shirin da ake yi na fada da ayyukan ta'addanci a nahiyar Afirka, kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta sanar da goyon bayanta ga dakarun hadin gwiwa na kasashen Yammacin Afirka a kokarin da suke yi na fada da kuma kawo karshen ayyukan ta'addancin kungiyar nan ta Boko Haram.

Kafafen watsa labarai sun bayyana cewar Smaїl Chergui, babban kwamishinan kwamitin sulhu da tsaron kungiyar Tarayyar Afirka, a wani taro da yayi da manyan kwamandojin dakarun hadin gwiwa na kasashen yammacin Afirkan kan fada da 'yan Boko Haram din ya gabatar da  wannan batun. Manufar wannan taron da aka gudanar da shi a birnin Addis Ababa helkwatar kungiyar Tarayyar Afirkan, kamar yadda a sanarwar bayan taron aka sanar, ita ce tattaunawa kan yanayin tsaro a yankin da kuma tasirin ayyukan dakarun hadin gwiwa na kasashen yankin da suka hada da Nijeriya, Nijar, Chadi da Kamaru.

Manufar kafa dakarun hadin gwiwa din dai wanda shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ba da shawarar kafawa ita ce fada da kungiyar Boko Haram da kuma kawo karshen ayyukan ta'addanci da take yi a yankin, lamarin da ya sanya ya zuwa yanzu dai ana iya cewa dakarun sun sami nasarar raunana karfin 'yan kungiyar  ta Boko Haram nesa ba kusa ba.

Kwamtinin sulhu da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirkan, wanda alhakin taimako wajen  tabbatar da tsaro da zaman lafiyan kasashe membobin kungiyar  Tarayyar Afirka yake wuyansa, ya kafa wani kwamiti da ya kumshi kwamandojin dakarun hadin gwiwan kasashen Yammacin Afirkan, mataimakan kwamandojin da sauran jami'ai da ke da helkwata a kasar Chadi duk dai don cimma wannan manufa ta kawo karshen ayyukan 'yan Boko Haram din. Don haka ne masana suke ganin irin wannan goyon baya na kwamitin zai taimaka wajen karfafa wa dakarun hadin gwiwan kasashen yammacin Afirkan gwiwa wajen ci gaba da wannan gagarumin aiki da aka dora musu.

Manufar kafa wadannan runduna dai ita ce samar da hadin gwiwa da aiki tare tsakanin rundunonin sojin kasashen Yammacin Afirkan a ci gaba da fada da ake yi da kungiyar ta Boko Haram. Hakan kuwa yana daga cikin kudurin da shugabannin kasashen Afirkan suka dauka ne na fada da kungiyoyin ta'addancin da suke gudanar da ayyukansu a kasashe daban-daban na nahiyar irin su Boko Haram a Nijeriya da Al-Shabab a Somaliya da sauransu don  tabbtar da tsaro da kwanciyar hankali a dukkanin nahiyar saboda alaka ta kut da kut da ke tsakanin tsaro da ci gaba da kuma karfafuwar tattalin arziki

A halin yanzu dai kasashe daban-daban na Afirkan irin su kasar Libiya, suna fuskantar matsaloli na tsaro daban-daban. Haka ne ma ya sanya a makon da ya wuce shugabannin kasashen da ke makwabataka da kasar Libiyan suka gudanar da wani taro a birnin Addis Ababa don tattaunawa kan halin da kasar Libiyan take ciki da kuma tattaunawa kan yadda za a magance wannan matsala ta rashin tsaro da ake guskanta.

Sakamakon irin ayyukan ta'addancin da kungiyoyin Boko Haram da Al-Shabab suke yi ba za a iya cewa hatsarin da ke tattare da wadannan kungiyoyi sun takaitu ga kasashen Nijeriya da Somaliya kawai ba ne, face dai hatsari ne da ke fuskantar kusan dukkanin kasashen nahiyar Afirkan musamman ma kasashen da suke makwabtaka da wadannan kasashe biyun da su ne tushen wadannan kungiyoyi biyu na ta'addanci.

A saboda haka ne masana suke ganin hadin gwiwa tsakanin kasashen nahiyar Afirkan wani lamari ne da ya zama wajibi wajen fada da wadannan kungiyoyi na ta'addanci da masa wasunsu.