Fiye Da jami'an Sojin Libya 20 Ne Suka Rasa Rayukansu A Benghazi
A wani bata kashi da aka yi tsakanin dakarun gwamnatin kasar Libya da kuma 'yan ta'adda, an kashe dakarun Libya 20 tare da jikkata wasu fiye da 40 a garin Benghazi.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, tun kimanin kwanaki biyu da suka gabata ne aka fara artabun tsakanin jami'an soji da ke biyya ga gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita a Libya, da kuma 'yan ta'adda a daya bangaren da ke dauke da akidar wahabiyyah takfiriyyah.
Tun kafin lokacin da kungiyar ISIS ta kwace iko da wasu muhimman wurare a gabashin kasar ta Libya, da suka hada da birnin Sirte birni na uku mafi girma a Libya, inda kuma daga bisani kungiyar take ta yunkurin kara fadada wuraren da take son mayar da su karkashin ikonta, musamman ma wurare masu arzikin danyen man fetur da ke gabashin kasar ta Libya.