Sojojin Gabacin Kasar Libya Sun Kwato Wasu Yankuna Daga Hannun Yan Ta'adda
Sojojin kasar Libya karkashin Janaral Khalifa Haftar sun sami nasarar kwato wasu yankuna daga hannu yan ta'adda a birnin Bengazi na gabacin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa majiyar watsa labarin ta sojojin Kalifa Haftar ne suka bayyana wannan labarin a jiya Alhamis, sannan labarin ya kara da cewa a halin yanzu umguwar Alkawasha na birnin Bengazi ta koma karkashin ikon sojojin sannan a fafatawarsu da yan ta'addan a jiya dun rasa sojoji 18 a yayinda wasu 54 suka ji rauni.
Labarin ya kara da cewa sojojinsu 4 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom a kan hanyarsu a yankin. Unguwar Alkawasha dai daya ne daga cikin sansanonin kungiyar Daesh a birnin na Bengazi, kuma yana da tazarar kilomiya goma daga tsakiyar birnin.
A ranar Laraba ma, wata majiyar ta fadawa Reuters cewa a fafatawar sojojin Haftar da yan ta'adda a birnin na Bengazi sojoji 20 ne suka rasa rayukansu a yayanda wasu 40 suka ji rauni.
Tun fiye da shekaru biyu da suka gabata yan ta'adda ta kunkiyar Daesh suke fafatawa da sojojin Khalifa Haftar a birnin na Bengazi.