'Yan Sandan Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 6 A Maiduguri
Rundunar 'yan sandan jihar Borno sun tabbatar da mutuwar mutane 6 sakamakon fashewar wasu tagwayen abubuwa a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Bornon Nijeriya.
Kafar watsa labaran nan ta Premium Times da ke watsa labaranta ta hanyar Internet ta jiyo majiyar 'yan sandan jihar Borno tana cewa wasu mutane shida sun rasa rayukansu a yayin da wasu ababe masu fashewa suka fashe a wajaje guda uku mabambanta a birnin Maiduguri a safiyar yau Juma'a.
'Yan sandan sun kara da cewa hudu daga cikin mutanen da suka mutun 'yan kungiyar Boko Haram ne saura biyun kuma dakarun sa kai ne na JTF.
'Yan sandan sun kara da cewa 'yan kunar bakin wake na farko din sun tarwatsa kansu ne a kusa da wani wajen bincike na jami'an tsaro kusa da babban kotun birnin Maiduguri. Sai kuma fashwar na biyu bayan da wani dan kunar bakin waken da suka kai harin sun yi kokarin shiga tashar motar Muna inda ya tarwatsa kansa kafin ya shiga cikin tashar. Sai kuma na uku wanda ya faru a kusa da wani wajen binciken.
Kwamishin 'yan sandan jihar Bornon ya kirayi al'ummar garin Maidugurin da su yi taka tsantsan.