An Sace Sakataren Ministan Harkokin Tsaron Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14161-an_sace_sakataren_ministan_harkokin_tsaron_gwamnatin_hadin_kan_kasar_libya
Wata majiyar labarai daga birnin Trabulus na kasar Libya ta bayyana cewa wasu yan bindiga wadanda har yanzun ba'a tantance ko suwaye ba sun sace sakataren ofishin ministan tsaron kasar ta Libya Mahdi Barguthy.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Nov 20, 2016 10:57 UTC
  • An Sace Sakataren Ministan Harkokin Tsaron Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya

Wata majiyar labarai daga birnin Trabulus na kasar Libya ta bayyana cewa wasu yan bindiga wadanda har yanzun ba'a tantance ko suwaye ba sun sace sakataren ofishin ministan tsaron kasar ta Libya Mahdi Barguthy.

Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran daga birnin Tarabulus ta bayyana cewa a jiya Asabar ne wasu yan bindiga wadan ba'a san ko su waye ba suka sace mutane 6 na kusa da ministan tsaron kasar Mahdi Albargusi. kuma har yanzun ba wanda ya san inda suke, ba waku wata kungiya ko jam'ar da ta bayyana cewa uta ce ta sace mutanen.

Banda haka a ranar Alhamis da ta gabata ma ofishin ministan ta bada labarin cewa ministan ya tsallaka rijiya da baya a wani kokarin da wasu yan bindiga suka yi na kashe shi. sai dai daya daga cikin masu tsaronsa ya ji rauni.

Kasar Libya dai tana fama da tashe tashen hankula tun bayan kissan shugaba Mu'ammar Kazzafi a shekara ta 2011.