Mutane Biyar Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Nakia A Arewacin Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1423-mutane_biyar_sun_mutu_sanadiyyar_tashin_nakia_a_arewacin_kamaru
Mutane biyar ne aka tabbatar da butuwarsu sanadiyyar taka nakiya wanda motarsu tayi a wani wuri a Arewacin kamaru a yau Lahadi. Kamfanin dillancin labaran
(last modified 2018-08-22T11:27:52+00:00 )
Feb 28, 2016 17:17 UTC
  • Mutane Biyar Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Nakia A Arewacin Kamaru

Mutane biyar ne aka tabbatar da butuwarsu sanadiyyar taka nakiya wanda motarsu tayi a wani wuri a Arewacin kamaru a yau Lahadi. Kamfanin dillancin labaran

Mutane biyar ne aka tabbatar da butuwarsu sanadiyyar taka nakiya wanda motarsu tayi a wani wuri a Arewacin kamaru a yau Lahadi. Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya bayyana cewa hakan ya auku ne a wani wuri kilomita 30 daga garin Makary daga jihar Arewa mai nisa.

Labarin ya kara da cewa mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa kauyen Bungu ne daga Makary a lokacinda motarsu ta taka nakiyan da aka biszne a kan hanya, kuma a nan take mutane biyu suka mutu sannan saura ukku kuma sun mutu ne a kan hanyarsu ta zuwa asbiti.

Mutanen garin makary sun kauracewa garin tun da dadewa don yawan hare haren da mayakan boko haram suke kai wa a garin. Duk da cewa ba'a ji ta bakin jami'an tsaro a yankin ba. Amma yatsun tuhuma suna nuni ne ga kungiyar boko haram da bizne wadan nan nakiyoyi. Jami'an tsaron kasar da dama da kuma mayakan sa kai na cikin mutane sun rasa rayukansu sanadiyyar tashin nakiyoyi da kuma hare haren boko haram a yankin arewa mai nisa na kasar camaroo.