Mutane 4 sun rasu a zanga-zangar malaman makaranta a Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14308-mutane_4_sun_rasu_a_zanga_zangar_malaman_makaranta_a_kamaru
Zanga-zangar maliman makaranta ta yi sanadiyar mutuwar mutane 4 a garin bamenda na yammancin kasar Kamaru
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Nov 23, 2016 14:40 UTC
  • Mutane 4 sun rasu a zanga-zangar malaman makaranta a Kamaru

Zanga-zangar maliman makaranta ta yi sanadiyar mutuwar mutane 4 a garin bamenda na yammancin kasar Kamaru

A ranar talatar da ta gabata maliman makarantun boko sun gudanar da zanga zanga domin nuna adawar su kan umarnin lauyoyi na fassara Dokokin kasar da yaran Faransanci

Jami'an tsaro sun yi harbi da alburushi da jefa barkonon tsohuwa ga masu yin zanga-zanga, wadanda suka zargi gwamnati da hade yankin da ake amfani da harshen Ingilishi. Yawancin Kamaru na amfani da harshen Faransanci ne.

Lauyoyi da malamai na adawa kan tilasta musu yin amfani da Faransanci a yankin da ake magana da harshen Faransanci da Turanci a garin Bamenda da ke Kamaru.Shugaban jam'iyar adawa ta Social Democratic Front, John Fru Ndi wanda aka haifa a Kudu maso Arewacin kasar, ya ce mutum hudu ne suka mutu a yayin zanga-zangar.

Fada ya barke ne bayan da kungiyar malamai ta Kamaru ta yi kiran zanga-zanga kan yadda harshen Faransanci ya mamaye harkar koyarwa a makarantu fiye da harshen Ingilishi.

Rashin jituwa ya barke tsakanin masu amfani da harshen Ingilishi da na Faransa a wasu sassan kasar, inda lauyoyi suka bukaci a fassara dokokin kasar zuwa harshen Ingilishi.

A bangare guda,Kamfanin dillancin Labaran Afirka News ya nakalto Majiyar tsaron kasar Kamaru a wannan Laraba na cewa Ma'aikatar tsaron kasar ta fara tura karin yawan dakarun ta a yankunan iyakar kasar da yankin Kogin Chadi, bayan harin da kungiyar boko haram ta kai  sansanin sojin kasar dake yankin a jiya Talata inda suka kashe Sojojin Chadin guda 6.

Har ila yau, Majiyar tsaro da Majalisar Dinkin Duniya sun sanar da cewa wani gungu da mayakan boko haram din da iyalan su sun meka kansu ga Dakarun tsaron kasar ta Kamaru.