An karfafa matakan tsaro a kasar Kamaru
Majiyar tsaron Kamaru ta karfafa matakan tsaro a yankunan iyakar kasar bayan harin da 'yan boko haram suka kai a sansanin Dakarun tsaron kasar dake yankin kogin Chadi
Kamfanin dillancin Labaran Afirka News ya nakalto Majiyar tsaron kasar Kamaru a wannan Laraba na cewa Ma'aikatar tsaron kasar ta fara tura karin yawan dakarun ta a yankunan iyakar kasar da yankin Kogin Chadi, bayan harin da kungiyar boko haram ta kai sansanin sojin kasar dake yankin a jiya Talata inda suka kashe Sojojin Chadin guda 6.
Har ila yau, Majiyar tsaro da Majalisar Dinkin Duniya sun sanar da cewa wani gungu da mayakan boko haram din da iyalan su sun meka kansu ga Dakarun tsaron kasar ta Kamaru.
A bangare guda kimanmin mutane 4 ne suka rasa rayukansu sanadiyar barkewar rikici tsakanin masu amfani da harshen Faransanci da kuma Turanci a yankin Bamenda dake arewacin kasar, bayan da kungiyar malamai ta Kamaru ta yi kiran zanga-zanga kan yadda harshen Faransanci ya mamaye harkar koyarwa a makarantu fiye da harshen Ingilishi.
Lauyoyi da malamai na adawa kan tilasta musu yin amfani da Faransanci a yankin da ake magana da harshen Faransanci da Turanci.
Shugaban jam'iyar adawa ta Social Democratic Front, John Fru Ndi wanda aka haifa a Kudu maso Arewacin kasar, ya ce mutum hudu ne suka mutu a yayin zanga-zangar.