Mata Yan Kunan Bakin Waki Biyu Sun Kai Hari A Kasar Kamaru
Yan mata biyu yan kudan bakin wake sun kai hari a wani gari a arewa mai nisa na kasar kasar a safiyar yau Alhamis.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan matan 2 masu shekaru tsakanin 13 da 18 sun shigo garin Mora da ke kan iyaka da tarayyar Nigeria ne a safiyar yau Alhamid wanda kuma ya kasance ranar kasuwace a garin.
Labarin ya kara da cewa daya daga cikin yan matan ta tarwatsa kanta a cikin mutane a kasuwar amma ita kadai ta muta bayan da ta ji wa wasu da dama rauni. Sannan mutane suka kashe dayar kafin ta tada boma bomata.
Wani jami'in hukuma a ma'aikatar Mayo-Sava wanda kuma ya ganewa idanunsa abinda ya faru, mai suna Babila Akawu ya fadawa reuters cewa wannan shi ne hari na hudu a wannan mako a yankin. Ana tuhuman kungiyar yan ta'adda ta Bokom Haram wacce take ayyukanta tsakanin kasashen Niger Nigeria Kamaru da Chadi da shirya hare haren.