Wasu Mata 'Yan Kunar Bakin Sun Kai Hari Arewacin Kasar Kamaru
Mahukunta a kasar Kamaru sun sanar da cewa wasu mata budurwaye 'yan kunar bakin wake sun kai wani hari a garin Mora da ke lardin Arewa mai nisa na kasar, hakan shi ne irin sa na hudu da 'yan ta'addan suka kai kasar Kamarun cikin mako guda.
Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo wani jami'in lardin mai suna Babila Akaou yana fadin cewa daya daga cikin bama-baman ya tarwatse ne a garin na Mora inda daya daga cikin mata maharar ta mutu kana wasu guda hudu kuma sun sami raunuka.
Har ila yau jami'in ya kara da cewa mace ta biyun ta mutu ne bayan da mutane yankin suka mata dukar kawo wuka a lokacin da suka fahimci tana kokarin tada bam din da ke jikinta.
Su dai wadannan 'yan matan da aka ce 'yan shekaru kimanin 13 da 18 ne sun shigo garin ne da nufin tarwatsa kansu a cikin kasuwa a daidai lokacin da jama'a suka taru don cin kasuwa.
Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram sun kai munanan hare-hare kasar ta Kamaru ta hanyar amfani da hare-haren kunar bakin wake.
Kasar Kamaru din dai tana daga cikin kasashen yankin da suka hada da Nijeriya, Nijar da Chadi da suka kaddamar da dakarun hadin kai da nufin ganin bayan kungiyar ta Boko Haram da ta kasance musu babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar al'ummar kasashen.