Demokradiyyar Congo: Barazanar "Yan tawayen Kasar Uganda Na Karuwa.
Fada Mai Tsakanin 'Yan tawayen kasar Uganda da sojojin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
An yi fada mai tsanani a tsakanin kungiyar 'yan tawayen kasar Uganda da ake kira ( United Democratic Forces) da kuma sojojin kasar Jamhuriyar demokradiyyar congo.
Cibiyar watsa labaru ta Africa Times, ta ambaci cewa; Fadan da aka yi a yankin arewacin kasar, a watan da ya shude kadai, ya ci rayuka da kuma jikkata mutane 400.
Sojojin kasar ta Demokradiyyar dai suna kokarin korar 'yan tawayen kasar ta Uganda ne daga garuruwan da su ke iko da su a cikin kasar.
"Yan tawayen kasar ta Uganda da su ke kokarin kifar da gwamnatin shugaban Yuweri Museveni, suna da sansanin a cikin dazukan kasar jamhuriyar demokradiyyar Congo.