An Fara Taron Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa A Kasar Tunisa
A jiya talata ce aka fara taron kasa da kasa na farfodo da tattalin arzikin kasar Tunisa a birnin Tunis babban birnin kasar.
Tashar radio ta kasa da kasa ta kasar Faransa ta bayyana cewa taron mai taken Tunisa 2020 ya sami halattan manya manyan cibiyoyin tattalin arziki a duniya. Daga cikin wadan nan cibiyoyi sun hada da Bank Duniya, Bankin Turai na zuba jari, Bankin raya kasana Afrika da kuma wakilan na cibiyoyin tattalin arziki na kasashen Asia ta Turai da dama.
Banda haka akwai cibiyoyin zuba jari masu zaman kansu daban daban daga kasashen duniya da dama suke halattan taron.
Taron Tunisia 2020 dai zata tattauna yadda za'a fitar da kasar daga matsalolin tattalin arzikin da ta fada ciki tun bayan juyin juya halin kasar a shekara ta 2011. Kuma a shekara ta 2015 kasar ta fada cikin rikicin ayyukan ta'addanci wanda ya karya gadon bayan tattalin arkin kasar wanda shi ne yawon shakatawa. Hakan dai ya kara yawan marasa aikin yi ya kuma kara jefa kasar cikin lullumi.