An Fara Shari'ar Magudun Juyin Mulkin Sojan Kasar Mali, Sanogo
(last modified Thu, 01 Dec 2016 06:25:06 GMT )
Dec 01, 2016 06:25 UTC
  • An Fara Shari'ar Magudun Juyin Mulkin Sojan Kasar Mali, Sanogo

Rahotanni daga kasar Mali sun bayyana cewar an fara shari'a wa shugaban juyin mulkin soji na kasar Kyaftin Amadou Sanogo da wasu mukarrabansa su 17 a garin Sikasso da ke kimanin kilomita 300 daga babban birnin kasar, Bamako bisa zargin kisan wasu sojojin da suke gadin fadar shugaban kasa.

A yayin da aka shigo da shi kotun Kyaftin Amadou Sanogo, ya bayyana cewar yana cikin koshin lafiya da kuma karfin gwiwan yana mai cewa daman yana jiran wannan rana ce da za a gurfanar da shi a gaban kotun don yi masa shari'ar.

A watan Maris na shekara ta 2012 ne dai Kyaftin Sanogo ya jagoranci wani juyin mulki na soji don kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Ahmadou Toumani Toure lamarin da ya sanya kasar Mali din cikin yanayi na rikici na siyasa abin da ya ba wa Buzaye 'yan tawaye da kuma wasu masu tsaurin ra'ayin addini kwace wasu yankuna na kasar daga hannun dakarun gwamnati. Daga baya dai Sanogo ya mika mulki ga gwamnatin farar hula.

A watan Disamban 2013 ne dai aka kama Kyaftin Sanogo bisa zargi kashe wasu sojojin masu gadin fadar shugaban kasar su 21 wadanda suka ki amincewa da juyin mulkin nasa. Daga karshe dai an sami gawawwakin wadannan sojoji a bisne a wani kabari na gama gari kusa da helkwatar sansanin sojojin Sanogo dake garin Kati.

An dage shari'ar dai har sai zuwa ranar Juma'a mai zuwa. Idan aka same shi da laifi yana iya fuskantar hukumcin kisa.