Ana ci gaba da gumurzu a arewacin Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14713-ana_ci_gaba_da_gumurzu_a_arewacin_mali
Akalla Mutane biyu ne suka rasu yayin wani gumurzu tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai a arewacin kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T11:29:20+00:00 )
Dec 02, 2016 11:20 UTC
  • Ana ci gaba da gumurzu a arewacin Mali

Akalla Mutane biyu ne suka rasu yayin wani gumurzu tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai a arewacin kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto mahuntar kasar Mali a jiya Alkhamis na cewa Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama na daban suka jikkata a yayin wani fada tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai a birnin Gao dake arewacin kasar .

Rahoton ya ce an dakatar da duk wata zirga-zirga a filin sauka da tashin na jiragen saman birnin sakamakon rokokin da ake halbawa a filin jirgin.

A ranar Larabar da ta gabata ma mahukuntan kasar sun sanar da tarwatsewa bama-bamai da aka sanya a wasu manya motoci guda biyu a filin sauka da tashi na jiragen saman birnin na Gao.

Har ya zuwa yanzu Gwamnatin ta Mali ba ta kasa cimma nasarar zartar da yarjejjeniyar sulhun 2015 din da aka cimma tsakanin ta da kungiyoyin 'yan tawayen arewacin kasar, lamarin da ya sanya ake ci gaba da tashin hankali a arewacin kasar.