Goyon bayan ayyukan MDD a kasar Mali
Kwamandan Dakarun wanzar da Zaman Lafiya na MDD a Mali ya bayyana samun Nasara a fagen yaki da ta'addanci
Kafar watsa labaran Afirka time ya nakalto Michael Lollesgaard babban Kwamandan Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya watau Munusma yayin da yake jawabi na kawo karshen aikinsa ya mayar da martani kan masu suka kan ayyukan Dakarun na Amison , inda ya ce Dakarun wanzar da zaman lafiyar sun yi aikinsu kamar yadda ake bukata domin sun yi kokari sosai wajen kare fararen hula a kasar ta Mali.
Kwamandan ya kara da cewa domin tunkarar aiyukan ta'addanci dole ne Dakarun wanzar da zaman lafiyan su yi aiki fiye da wanda suka yi a baya.
Duk da irin hare-haren ta'addancin da ake kaiwa fararen hula a baya-bayan nan Michael Lollesgaard ya bayyana aikin Dakarun na sa da samun nasara a kan ta'addanci.