Shugaba Jammeh Ya Ce Zai Girmama Abin Da Al'ummar Kasar Suke So
(last modified Sat, 03 Dec 2016 18:05:09 GMT )
Dec 03, 2016 18:05 UTC
  • Shugaba Jammeh Ya Ce Zai Girmama Abin Da Al'ummar Kasar Suke So

Shugaban kasar Gambia mai barin gado Yahya Jammeh ya bayyana cewar zai ci gaba da amincewa da zabin al’ummar kasar sakamakon kayen da ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata inda aka sanar da madugun 'yan hamayyar kasar Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben.

Shugaba Jammeh ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi wa al'ummar kasar Gambiyan ta gidan talabijin din kasar inda ya bayyana amincewarsa da sakamakon zaben da kuma taya sabon shugaba Adama Barrow murnar wannan nasara da ya samu yana mai masa da kuma al'ummar kasar fatan alheri.

Har ila yau shugaba Jammeh ya ce a shirye ya ke yayin aiki da sabon shugaban matukar yana son hakan wajen ganin an ciyar da kasar gaba da kuma da kuma ganin an mika mulkin cikin nasara, lamarin da ya ke nuni da cewa ba shi da aniyar kalubalantar sakamakon zaben.

A jiya Juma'a ne dai shugaban hukumar zabe na kasar Gambiyan ya sanar da Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar lamarin da zai kawo karshen mulkin shugaba Yahya Jammeh na tsawon shekaru 22 a kasar.