An kafa Dokar ta bace a kasar Libiya
Dakarun tsaron Libiya sun kafa dokar ta bace a fadin kasar gaba daya.
A yayin da yake tattaunawa tare da 'yan jaridu Shugaban Majalisar Gwamnatin hadin kan kasar Libiya Ali Kartani ya bayyana cewa an kafa dokar ta bacen ne da nufin dunkule ma'aikatun kasar wuri daya ne.kuma a yayin dokar ta bacen dukkanin Ma'aikatun Gwamnatin , in banda Majalisar Dokokin kasar za su kasance kalkashin kulawar Sojoji har lokacin da yanayi ya koma kamar yadda yake a baya.
Wannan doka na zuwa ne a yayin da Sojojin kasar suka tsarkake garin Sirte daga 'yan ta'addar ISIS,Kakakin rundunar sojin Libya Reda Issa, ya tabbatar da samun nasarar da sojojin kasar suka samu a garin Sirte inda ya kara da cewa ayukan sojoji masu biyayya da dama sun salwanta yayin fafutukar ganin sun kwato birnin na Sirte da ke a matsayin tunga mafi karfi ta mayakan IS a Libya.