Jam'iyyar Shugaba Jammeh Ta Shigar Da Kara Kan Sakamakon Zaben Shugaban Kasar
(last modified Wed, 14 Dec 2016 11:07:05 GMT )
Dec 14, 2016 11:07 UTC
  • Jam'iyyar Shugaba Jammeh Ta Shigar Da Kara Kan Sakamakon Zaben Shugaban Kasar

A daidai lokacin da alamu suke nuni da rashin nasarar kokarin shiga tsakanin da kungiyar ECOWAS ta tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka take yi don magance rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar Gambiya, jam'iyyar APRC mai mulki a kasar ta shigar da kara tana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar ta sanar inda ta ce shugaba Yahya Jammeh ya sha kaye.

Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin Banjul, babban birnin kasar Gambiya ya ba da labarin cewa Jam'iyyar Alliance for Patriotic Reorientation and Construction (APRC) mai mulki ta shigar da karar ne a jiya Talata, wacce ita ce ranar karshe da kundin tsarin mulkin kasar ya bayar na shigar da korafi kan sakamakon zaben, inda take kalubalantar sakamakon zaben da aka sanar din da ke nuni da dan takarar 'yan adawar kasar Adama Barrow shi ne ya lashe zaben, inda take zargin cewa an tafka magudi a yayin zaben.

A bangare guda kuma wasu rahotannin suna nuni jami'an tsaron kasar sun mamaye helkwatar hukumar zaben kasar da hana ma'aikatar wajen gudanar da ayyukansu ciki kuwa har da shugaban hukumar zaben Alieu Momar Njai.

A jiya ne dai wasu shugabannin Afirka da suka hada da Muhammadu Buhari na Nijeriya, John Dramani Mahama na Ghana da Ernest Bai Koroma na Saliyo karkashin jagorancin shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf suka isa kasar Gambiya don tattaunawa da shugaba Jammeh da shugaba mai jiran gadon Adama Barrow kan samun hanyar da za a magance rikicin.