An gano wasu shaidun ta'addanci a jiragen kasar Masar
(last modified Fri, 16 Dec 2016 06:28:53 GMT )
Dec 16, 2016 06:28 UTC
  • An gano wasu shaidun ta'addanci a jiragen kasar Masar

A farkon tsakiyar shekarar 2016 Jiragen Masar sun fadi dalilin harin ta'addanci.

Kamfanin dillancin Labarai na Reuteus ya habarta cewa Kwamitin binciken da aka kafa kan faduwar jirgen Fasinja Kirar A 320 mallakin kasar Masar wanda ya fadi a tekun Meditarenia , a marecen jiya Alkhamis ya sanar da cewa ya gano ababen fashewa a cikin jirgin.

Kwamitin ya ce sun bayar da wannan dalilan ne bisa rahoton da Likitoci suka bayar na tabbatar da cewa gawawwakin da aka samu na fasinjan jirgin a kwai abeben fashewa a cikin su.

Bayan fitar da wannan rahoto, a kwai yiyuwar cewa akwai 'yan ta'adda da suka tarwatsa jirgen fasinjan na Masar.a watan Mayun da ya gabata ne jirgin Masar dauke da fasinja 66 da ya taso daga birnin Paris na kasar Faransa ya fadi a tekun Mediterainya, kuma dukkanin fasinjan dake cikin sa sun mutu.