An bukaci Sulhu a tsakanin 'yan kasar Libiya
Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musaman kan kasar Libiya ya bukaci dukkanin bangarorin Siyasar kasar da su yi sulhu a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Martin Kobler Manzon musaman na MDD kan kasar Libiya a wannan Lahadi na cewa sulhu tsakanin Al'ummar kasar Libiya ita ce mafita daya cilo da za ta kawo karshen halin da kasar ke ciki a yanzu, musaman ma a yayin da Dakarun hadin kan kasar suka fatattaki 'yan ta'addar ISIS daga birnin Sirte.
Mista Martin Kobler ya ce wajibi Al'ummar kasar ta Libiya su yi sulhu a tsakanin su.yayin da ya koma kan maganar 'yan gudun hijra na garin Sirte ya ce wajibi ne a tsarkake garin daga irin bama-baman da 'yan ta'adda suka dasa kafin su koma gidajen su.
Bayan kwashe sama da watani takwas ana fafatawa tsakanin Dakarun hadin kan kasar Libiya da kuma 'yan ta'addar ISIS, daga karshe Dakarun tsaron kasar sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'addar daga birnin, kuma wannan babbar faduwa ce ga 'yan ta'addar na ISIS da masu goya musu baya, babbar nasara ce kuma ga Al'ummar kasar ta Libiya.