Mutane 2 Sun Mutu Sakamakon Kunar Bakin Wake A Kasar Kamaru
Rahotanni daga kasar Kamaru sun bayyana cewar wasu mutane biyu sun rasa rayukansu kana wasu mutane biyar sun sami raunuka biyo bayan wani harin ta'addancin da aka kai wata kasuwa da take cike da jama'a a a garin Mora na kasar Kamarun.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wani na kurkusa da gwamnan lardin Arewa mai nisa na kasar Kamarun Midjiyawa Bakary yana fadin cewa harin dai na kunar bakin wake ne da wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai shi a garin na Mora inda mutane biyu, wani dalibi da wata mace suka rasa rayukansu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan Boko Haram din suke kai hari garin na Mora da ke kimanin kilomita 30 daga kan iyakar kasar Kamarun da Nijeriya ba.
Tun dai bayan da gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da hare-hare kan 'yan Boko Haram din da nufin kawo karshensu da dama daga cikinsu suka gudu zuwa kasashen da suke makwabtaka da Nijeriyan ciki kuwa har da kasar Kamarun suna aiwatar da ayyukansu a can.