Sojoji Sun Bar Hedikwatar Hukumar Zaben Kasar Gambiya
Rahotanni daga kasar Gambiya sun bayyana cewar sojojin kasar sun bar hedikwatar hukumar zaben kasar bayan mamaye wajen da suka yi na sama da makonni biyu da kuma korar ma'aikatan da suke wajen.
Rahotannin sun ce janyewar sojojin dai ta biyo bayan wata doka ce da gwamnatin ta fitar inda ta ce dukkanin ma'aikatan hukumar zaben suna iya komawa bakin aikinsu, tana mai cewa rufe hukumar zaben ma ya biyo bayan barazana ta tsaro ne da hedikwatar yake fuskanta a kokarin da wasu suka yi na kona shi.
A ranar 13 ga watan Disamban nan ne dai sojojin suka mamaye hedikwatar hukumar zaben kwanaki hudu bayan da shugaban kasar Yahya Jammeh ya sanar da rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 1 ga watan Disamban inda hukumar zaben ta sanar da cewa ya sha kaye a zaben.
Kasashe da cibiyoyin kasa da kasa dai sun yi Allah wadai da mamaye hedikwatar hukumar zaben da sojojin suka yi, kamar yadda kuma suke ci gaba da kiran shugaba Jammeh da ya mika mulki ga zababben shugaban da aka zaba wato Adama Barrow bayan karewar wa'adin mulkinsa, lamarin da har ya zuwa yanzu shugaban ya ce ba za ta sabu ba.