Mataimakin Shugaban Kasa Ta Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya Ya Ajiye Mukaminsa.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16036-mataimakin_shugaban_kasa_ta_gwamnatin_hadin_kan_kasar_libya_ya_ajiye_mukaminsa.
Mataimakin shugaban Kasa ta gwamnatin hadin kan kasa a kasar Libya ya ajiye mukaminsa, a jiya Litinin ya kuma bukaci afwa daga mutanen kasar kan kurakuran da ya aikata.
(last modified 2018-08-22T06:59:28+00:00 )
Jan 03, 2017 03:53 UTC
  • Mataimakin Shugaban Kasa Ta Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya Ya Ajiye Mukaminsa.

Mataimakin shugaban Kasa ta gwamnatin hadin kan kasa a kasar Libya ya ajiye mukaminsa, a jiya Litinin ya kuma bukaci afwa daga mutanen kasar kan kurakuran da ya aikata.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran daga birnin Tarabulus hedkwatar gwamnatin hadin kan kasar ta Libya ta bayyana cewa Musa Kani ya sauka daga kan mukaminsa ne bayan zargin lalata dukiyar gwamnati da fasa kori da kuma wasu manya manyan kura kurai a lokacinda yake rike da mukamin na mataimakin shugaban kasa. 

Kani dai ya zama mataimakin shugaban kasa ne tun watan maris na shekara da ta gabata. Labarin ya kara da cewa banda Musa Kani akwai wani yan majalisar ministocin kasar guda biyu  Ali Qarrani da kuma Umar Al-Asood wadanda aka dakatar da su daga aiki.

Kasar Libya dai tana fada da tashe tashen hankula tun faduwar gwamnatin Mu'ammar Kazzafi a shekara ta 2011.