Libya: Halifa Haftar Ya Ki Yin Sulhu Da Gwamnatin Hadin Kan Kasa.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16120-libya_halifa_haftar_ya_ki_yin_sulhu_da_gwamnatin_hadin_kan_kasa.
Kwamandan sojojin kasar ta Libya a gabacin kasar ya yi watsi da duk wani yunkurin sulhu da gwamnatin hadin kan kasa.
(last modified 2018-08-22T06:59:29+00:00 )
Jan 05, 2017 03:53 UTC
  • Libya: Halifa Haftar Ya Ki Yin Sulhu Da Gwamnatin Hadin Kan Kasa.

Kwamandan sojojin kasar ta Libya a gabacin kasar ya yi watsi da duk wani yunkurin sulhu da gwamnatin hadin kan kasa.

Kwamandan sojojin kasar ta Libya a gabacin kasar ya yi watsi da duk wani yunkurin sulhu da gwamnatin hadin kan kasa.

Halifa Haftar ya ce; Shekaru biyu da su ka gabata an yi tattaunawa da Fa'iz Suraj wanda shi ne Pira ministan gwamnatin hadin kan kasa a yanzu, amma babu wani sakamako da ya haifar, kuma har yanzu kasar babu abinda ya sauya.

Haftar ya kara da cewa a halin da ake ciki a yanzu, mayakansa ne su ke rike da kaso 80% na kasar ta Libya.

Bangarorin da su ke da sabani da juna a kasar Libya sun bude tattaunawa a kasar Aljeriya domin fahimtar juna da kawo karshen rikicin kasar.