Chadi Ta Rufe Iyakokinta Da Kasar Libya
(last modified Fri, 06 Jan 2017 05:17:11 GMT )
Jan 06, 2017 05:17 UTC
  • Chadi Ta Rufe Iyakokinta  Da Kasar Libya

Gwamnatin kasar Chadi ta sanar da rufe iyakokinta da kasar Libya, domin kaucewa kwararowar 'yan ta'adda daga Libya zuwa cikin kasarta.

Firayi ministan kasar ta Chadi Albert Pahimi Padacké ne ya sanar da hakan a jiya Alhamis a wani jawabinsa wanda gidajen radio da talabijin na kasar Chadi suka watsa kai daga birnin Njamina, inda ya ce Chadi ta dauki wannan matakin ne daga bangarenta saboda dalilai na tsaro.

Albert Pahimi Padacké ya kara da cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata wasu 'yan ta'adda sun karato iyakokin kasar Chadi daga kasar Libya, wanda  acewarsa hakan yana a matsayin wata babbar barazana ta tsaro ga kasar Chadi, kuma daukar matakin rufe iyakokin kasar da Libya shi kadai ne mafita domin kaucewa afkuwar hakan.