Masar: An kashe Sojan Masar Guda A Yankin Sina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16246-masar_an_kashe_sojan_masar_guda_a_yankin_sina
Masu dauke da makamai sun kashe wani sojan masar guda a yankin Sina ta arewa.
(last modified 2018-08-22T11:29:30+00:00 )
Jan 07, 2017 19:13 UTC
  • Masar: An kashe Sojan Masar Guda A Yankin Sina

Masu dauke da makamai sun kashe wani sojan masar guda a yankin Sina ta arewa.

Masu dauke da makamai sun kashe wani sojan masar guda a yankin Sina ta arewa.

Kamfanin dillancin Labarun "Irna" ya ambato wata majiyar tsaro daga kasar Masar na cewa; A yau asabar ne yan bindigar su ka kai farmaki akan wurin binciken soja da ke yankin Nakhal da ke tsakiyar gundumar sina ta arewa inda su ka kashe soja guda mai suna Mahmud Muhammad Jaudah dan shekaru 22.

Bugu da kari maharan sun jikkata wasu sojojin 4.

 A wani harin na daban,  da maharan su ka kai sojojin masar, sun  jikkata daya daga cikinsu a garin al-arish a gundumar ta Sina.

Kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai hare-haren sai dai yankin na Sina ya shahara da kai haren kungiyoyin da su ke damfare da alqaeda da Da'esh.