Aljeria ta yi galgadin daukan matakan Soja wajen magance rikicin Libiya
Kasar Aljeria ta yi galgadin daukan matakan Soja wajen magance rikicin kasar Libiya
Kamfanin dillanicn Labaran kasar Faransa ya nakalto Ministan harakokin wajen kasar Aljeria Ramtana Lamara a jiya Alkhamis na cewa matakin da kasashen Duniya ke son dauka kan kasar Libiya ba zai taimaka wajen magance rikicin kasar ba, har yanzu kasar sa na kan bakanta na warware rikicin ta hanyar tattaunawa.
Lamana ya ce matakin Soja babu abinda zai aifar face kisa da rusa kasar, kuma Aljeria za ta mutunta duk wata Gwamnatin da aka kafa bisa bukatar Al'ummar kasar Libiya.
Kimanin kwanaki 10 kenan da aka bayyana cewa kasashen Faransa, Amurka da kuma Burtaniya sun tura sojojin su zuwa kasar ta Libiya domin kwace madafun iko daga hanun Gwamnatin Tripoli.
Kasashen Yamman sun yi amfani da gamgamin yaki da kungiyar ISIS wajen jibke Dakarun su a Libiyan, inda suke cewa a shirye suke su tabbatar da tsaro matukar aka kafa Gwamnatin hadin kan kasa.