Libya: Masu Dauke Da Makamai Na Shirin Kwace Ma'aikatu Uku Na Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16537-libya_masu_dauke_da_makamai_na_shirin_kwace_ma'aikatu_uku_na_gwamnati
Gwamnatin Hadin Kan kasar Libya ta ce wasu masu dauke da makamai suna shirin kwace ma'aikatu uku a birnin Tripoli.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jan 13, 2017 02:16 UTC
  • Libya: Masu Dauke Da Makamai Na Shirin Kwace Ma'aikatu Uku Na Gwamnati

Gwamnatin Hadin Kan kasar Libya ta ce wasu masu dauke da makamai suna shirin kwace ma'aikatu uku a birnin Tripoli.

Gwamnatin Hadin Kan kasar  ta ce; wasu masu dauke da makamai sun yi shirin kwace ma'aikatu uku  a birnin Tripoli.

Kakakin gwamnatin kasar ta Libya, Ashrafi al-sulusy ya ce; Masu dauke da makaman suna da alaka da Khakifa Guwail,  wani dan siyasa wanda bai yarda da gwamnatin hadin kan kasar ba, kuma sun yi kokarin kwace ma'aikatun kwadago da shahidai da wadanda su ka bace, da su ke karkashin gwamnatin hadin kan kasa.

al-sulaisy ya ci gaba da cewa; Bayan da aka yi batakashi tsakanin maharan da sojojin gwamnati, an kore masu makaman.

Libya tana ci gaba da fuskantar rashin tsaro tun faduwar gwamnatin Kaddafi a 2011.