Ana Gudanar Zaman Shugabannin Afirka Da Faransa A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16582-ana_gudanar_zaman_shugabannin_afirka_da_faransa_a_mali
An fara gudanar da zaman shugabannin kasashen Afirka da Faransa karo na ashirin da bakwai a birnin Bamako na kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T06:59:32+00:00 )
Jan 14, 2017 08:35 UTC
  • Ana Gudanar Zaman Shugabannin Afirka Da Faransa A Mali

An fara gudanar da zaman shugabannin kasashen Afirka da Faransa karo na ashirin da bakwai a birnin Bamako na kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin Bamako ya bayar da rahoton cewa, shugabannin kasashe gami da wakilan gwamnatocin fiye da 30 ne na Afirka tare da Faransa suka fara gudanar da zaman na yau a birnin na Bamako.

Zaman taron na yau ya zo ne bayan taron share fage da ministocin harkokin wajen kasashen Afirka da Faransa a jiya Juma'a, inda a yau kuma za a gudanar da babban taron, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka danganci bunkasa harkokin tattalin arziki da kuma tsaro.