Boma Bomai Sun Tashi A Wani Sansanin Sojoji A Arewacin Kasar Mali
(last modified Wed, 18 Jan 2017 11:54:07 GMT )
Jan 18, 2017 11:54 UTC
  • Boma Bomai Sun Tashi A Wani Sansanin Sojoji A Arewacin Kasar Mali

Majiyoyin labarai daga kasar Mali sun bayyana cewa wasu boma bomai masu karfi sun tashi a wani sansanin sojojin kasar daga arewacin kasar kuma sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta IRan daga Bamako babban birnin kasar ta bayyana cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wani sansanin sojojin kasar dake garin Gao na arewacin kasar sanadiyarra tashin boma bomai a safiyar yau Laraba. 

Majiyoyin sun kara da cewa har yanzun ba'a tantanci yawan mutanen da suka rasa rayukansu ko suka ji rauni ba, kuma babu wata kungiya da ta dauki nauyin tada boma boman ba. Amma kungiyar Murabidoon ta Mukhtar bin Mukhtar ita ce ta saba kai hare hare irin wannan a arewacin kasar ta Mali.

Banda sojojin kasar dai majalisar dinkin duniya tana da dubban sojoji a arewacin kasar ta Mali inda suke yakar kungiyoyin yan ta'adda da kuma wasu masu neman warewa daga kasar tun shekara ta 2013