An Gano Gawakin Yan Ta'adda Fiye Da 100 A Arewacin Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16816-an_gano_gawakin_yan_ta'adda_fiye_da_100_a_arewacin_kasar_libya
Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa an gano daruruwan gawakin yayan kungiyar Daesh a birnin Sirt wanda aka kwace daga hannunsu a yan makonnin da suka gabata.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 19, 2017 08:16 UTC
  • An Gano Gawakin Yan Ta'adda Fiye Da 100 A Arewacin Kasar Libya

Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa an gano daruruwan gawakin yayan kungiyar Daesh a birnin Sirt wanda aka kwace daga hannunsu a yan makonnin da suka gabata.

Kakakin sojojin kasar ta Libya Mohammad Al_gasri ne ya bayyana haka a jiya Laraba ya kuma klara da cewa tun lokacinda aka kwace birnin daga hannunu a cikin yan makonninn da suka gabata an gano gawakinsu kimani 2500 sannan har yanzun akwai zaton cewa wasu daruruwan suna bisne karkashin tarkashen gine ginen da aka rusa a kansu. 

Al-gasri ya kammala da cewa babu wani dan kungiyar Daesh wadanda suka yi iko da birnin da ya fice zuwa waje, sai dai akwai yayan wannan kungiyar a kudancin kasar wanda zai dauki shekaru kafin a kawo karshen su a yankin .